ABNA24 : Haka kuma a cewar babu wata riba da Iran za ta samu a wani sabon rikici ko tsokona a halin yanzu.
Majid Takht-Ravanchi, ya ce, ko a lokacin gwamnatin AMurka da ta shude Iran, ba ta nuna bukatar shiga wani rikici ba da AMurka, duk da tsokanar da akayi ta ma ta.
Jakadan na Iran, a MDD, ya bayyna hakan ne yayin wata hira ta tashar talabijin ta Al Jazeera, kan cewa akwai yiyuwar wani sabin rikici ya barke tsakanin AMurka da Iran, musamman kan matakan da Iran ke dauka game da yarjejeniyar nukiliyar data cimma da manyan kasashen duniya.
342/